1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky na neman tallafin makamai a Turai

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
February 9, 2023

Shugaba Volodymyr Zelensky ya nuna tsananin bukatar samun makaman Turai masu cin dogon zango don tunkarar mamayar Rasha a daidai lokacin da yakin ya kusa cika shekara daya da farawa.

https://p.dw.com/p/4NGiJ
Frankreich | Präsident Macron empfängt Selenskyj und Bundeskanzler Scholz in Paris
Hoto: Sarah Meyssonnier/REUTERS

Makwanni biyu kafin cika shekara daya da fara fuskantar mamaya daga Rasha, shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine zai halarci taron kolin Kungiyar Tarayyar Turai da zai gudanar a wannan Alhamis, a ci gaba da kwarya-kwaryan zagayen da yake a kasashen yankin don neman goyon baya da tallafi da makamai.

Kamar yadda ya bukata daga gwamnatin Birtaniya da Faransa a yammacin jiya, Shugaba Zelensky na bayyana bukatar da ke akwai na taimakawa kasarsa da manyan rokoki da jiragen yaki masu cin dogon zango don tunkarar mamayar sojan Rasha a fagen daga.

Ko da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, sun kara jaddada matsaya guda na ci-gaba da taimaka wa Ukraine komai rintsi. Sai dai shugabannin ba su yi wani cikakken karin haske kan bukatar Zelensky ba na tura manyan tankokin yakin da jiragen da ya ke bukata a cikin hanzari ba.