COP26: Musayar yawu a kan sauyin yanayi
November 4, 2021A makon da ya gabata ne birnin Glasgow na Scotland a Birtaniya, ya karbi bakwancin kasashen duniya akalla 200 da suka soma taron koli na Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi wato COP26, da zummar ci gaba da tattauna yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris. Manufar babban taron ita ce na rage hayaki mai haddasa dimamar yanayi da duniya ke fuskanta zuwa kasa da digo biyu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa duniya na cikin wata mummunar barazana ta dimamar yanayi da ya zarta maki biyu da digo bakwai, lamarin da ya kai ta ga cewar dole sai an zage damntse. Ko baya ga Majalisar Dinkin Duniya kwararru kan yanayi da kungiyoyin rajin kare muhalli, sun yi ittifakin cewa matakan da duniya ke dauka a yanzu kan hayaki mai gurbata muhalli basu taka kara suka karya ba.