1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

'Yan bindiga sun kai Dagestan da ke Rasha

Suleiman Babayo MA
June 24, 2024

Harin ta'addanci ya hallaka fiye da mutane 15 a yankin kudancin Rasha inda hukumomi suka kaddamar da bincike tare da halaka biye daga cikin maharan.

https://p.dw.com/p/4hQ0d
Yankin Dagestan na Rasha da aka kai hari
Yankin Dagestan na Rasha da aka kai hariHoto: Gyanzhevi Gadzhibalayev/TASS/dpa/picture alliance

'Yan sanda da fararen hula fiye da 15 suka halaka cikin har da wani babban mai wa'azi na addinin Kitrista, lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki yankin Dagestan na kudancin kasar Rasha. Gwamnan yankin Sergei Melikov ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa a wani faifan bidiyo da ake sake a wannan Litinin. An kai hare-haren kan wasu majami'u guda biyu da wajen bauta na Yahudawa gami da wasu ofisoshin 'yan sanda lokaci guda.

Karin Bayani: Farautar 'yan Isra'ila a filin jirgin saman Dagestan

Hukumomin Rasha suna zargi harin na ta'addanci a wannan yankin da yake da mazauna galibi mabiya addinin Islama. Tuni rundunar yaki da ta'addaci ta Rasha ta bayana halaka biyar daga cikin 'yan bindiga da suka kai harin na wannan Lahadi da ta gabata.