1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila na son Antonio Guterres ya yi murabus

October 25, 2023

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga jagoran majalisar ta duniya Antonio Guterres da ya yi murabus, bayan matsayar Mr. Guterres kan halin da ake ciki a Gaza.

https://p.dw.com/p/4XzxP

Jakadan na Isra'ila, Gilad Erdan ya yi zargin Antonio Guterres ne da rashin dacewa da matsayin saboda abin da ya kira yarda da ya yi ta'addanci da kungiyar ke yi.

Cikin wasu kalaman da Antonio Guterres ya yi a Majalisar Dinkin Duniya a baya-bayan nan, ya nuna cewa da Isra'ila da kungiyar Hamas dukkaninsu sun taka dokokin kasa-da-kasa a rikicin da suke yi a tsakaninsu.

Antonio Guterres ya kuma ce matakin tsagaita bude wuta ne kadai zai kawo karshen wahalhalun da ake ciki a Zirin Gaza, kamar yadda hakan zai taimaka wajen samun damar sako wadanda Hamas ke garkuwa da su.

Shi ma ministan harkokin wajen Isra'ila, Eli Cohen ya soki Antonio Guterres tare da dakatar da wata ganawar da ya tsara yi da shi.

Isra'ila dai na ci gaba da hare-haren ramuwar gayya kan Zirin Gaza, bayan harin ranar 7 ga wannan wata na Oktoba da ya kashe sama da mutum 1,400 a kasar tare da garkuwa da wasu sama da 200.