SiyasaTurai
Italiya ta tsananta tsaro bayan harin Rasha
March 26, 2024Talla
An cimma matakin ne bayan taron majalisar manyan masu hannu cikin al'amuran tsaron kasar da aka yi a birnin Rome.
Tuni ma aka tsara manyan matakan tsaro a wannan mako da ake gab da fara hidindimun Easter da mabiya addinin Kirista ke girmamawa.
A irin wadannan lokutan, Paparoma Francis kan kasance da ayyuka masu yawan gaske masu nasaba da lokacin na Easter a Rome da kuma fadar Vatikan.
Kungiyar ta'adda a duniya IS ta ce ita ta kai harin harin.
Ita ma Jamus ta bakin ministan harkokin cikin gidanta, ta nuna cewa barazana daga kungiyoyi na ta'adda matsala ce gagaruma.
A karon farko dai Shugaba Putin na Rasha ya amince cewa harin na da alaka da 'yan ta'adda, ammam kuma ya danganta su da kasar Ukraine.