Kasashe masu karfin tattalin arziki na taro a Jamus
October 5, 2023Babba burin wannan Asusu da ake kira Green Climate shi ne tilasta wa kasashe masu ci gaban masana'antu biyan diyya ga kasashe matalauta da ke dandana radadin sauyin yanayi da kuma canja sheka izuwa amfanin makamashi mai tsafta wajen bunkasa tattalin arziki.
Karin bayani: Manufofin ci-gaba mai dorewa
Asusun dai na Green ya tanadi gudanar da tsare-tsare da ayyuka sama da 200 a matsayin tallafi musanman ma a nahiyar Afrika da Asiya da kuma Latin Amurka da kuma tsibirin Caraibes.
Karin bayani: AU za ta samar da dala biliyan 26 domin yaki da sauyin yanayi
Sai dai yayin da gabanin buda taron kasashen Tarayyar Turai da Burtaniya da Kanada da kuma Koriya ta Kudu suka sanar da ba da biliyoyin daloli, har yanzu Amurka ba ta ce ufan ba a game da tallafin da take sa ran bayar wa.