1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Joe Biden zai gurfana a gaban kotu

Abdourahamane Hassane
September 15, 2023

An tuhumi dan shugaban Amurka Joe Biden, Hunter Biden da laifin mallakar makami ba bisa ka'ida ba. Wannan shi ne karo na farko da dan shugaba mai ci a Amirka zai fuskkanci shari'a.

https://p.dw.com/p/4WMop
Dan shugaban Amirka Hunter Biden
Dan shugaban Amirka Hunter BidenHoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Lauyan mai shigar da kara na musamman da Atoni JanarMerrick Garland ya nada yana zargin dan shugaban kasar da boye gaskiyar cewa shi mai shan miyagun kwayoyi ne lokacin da ya siye makamin a shekara ta 2018.Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin Amurka da ake tuhumar dan wani shugaban kasa mai ci. Kuma idan har aka sameshi da laifin za a iya yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 na gidan jarum, Dan shekaru 53  Hunter mai  aiki a matsayin mai fafutuka da zuba jari zai iya kanacewa a gaban  kotu dab da lokacin da mahaifinsa Joe Biden ke shirin sake tsaya takara a zaben shugaban kasa na  amirka a badi.