Najeriya ta ce ba ta da wani shiri da Faransa kan Nijar
December 27, 2024Shugabangwamnatin Sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce gwamnatinsa na da muhimman bayanai na sirri da suka tabbatar da wannan zargi na kafa sansanin sojojin Faransa a yankin Tafkin Chadi wanda ya alakanata da kokarin da ake yin na wargaza zaman lafiyar kasarsa.
Shugaba Tiani ya kalubalanci hukumomin Najeriya bisa masaniya da yake da ita inda ya ce sun yi bincike za su tabbatar da maganar da gaskiyyar maganar. Yayin da wasu ‘yan kasar da ke zaune a yankin suka musanta wannan zargi wasu kuma na ganin a dai yi bincike ka da a yi saurin yanke hukuncin na rashin sansanin sojojin ko akasin haka. Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta wannan zargi da ta ce sam ba shi da tushe don kuwa ba za ta taba yin wani abu da zai shafi zaman lafiyar kasashen makobtanta ba.