1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kifar da gwamnatin Najeriya?

May 4, 2021

A cigaba da ka-ce-na-ce bisa batun tsaron Tarayyar Najeriya, mahukuntan kasar sun ce wasu da ba a ambato ko su wanene ba, na kokarin kai karshen gwamnati.

https://p.dw.com/p/3sxhX
Nigeria Katsina | Präsident Muhammadu Buhari
Zargin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Tun da farko dai rundunar sojan Najeriyar ta tabbatar da goyon baya ga kundin tsari da ma mulkin dimukuradiyyar cikin kasar a halin yanzu, kafin wata sanarwar fadar gwamnati da ta ce akwai alamun hadin baki na wasu da ke da niyyar kifar da gwamnatin kasa. Duk da cewar dai Abujar ba ta ambato sunaye ko kuma kungiyoyin da take zargi da kokari na kai karshen mulkin na masu tsintsiya ba dai, wannan ne karo na farko da ta fito fili tare da bayyana zargin da ke zaman mai nauyi.

Karin Bayani: Barazarar tsaro ga zabukan 2023 a Najeriya

A cikin tsakiyar ka-ce-na-cen da ke dada karfi dai, na zaman batun tsaron da ya raba kai a tsakanin masu ganin Abujar ta kasa da kuma masu yi wa batun tsaron kallo na idanu na siyasar da ke kara baki cikin kasar a halin yanzu. An dai ruwaito wani lauya a kudancin Najeryar yana fadin akwai bukatar shugaban kasar ya mika mulki ga rundunar sojojin da ita kuma za ta jagoranci rabuwar kasar zuwa gida Shida, ko bayan masu siyasa da malaman addini da muryarsu ke dada karfi cikin karatun sai an sauyar.

Nigeria I Überfall auf Gefängnis
Matsalar raashain tsaro na kara ta'azzara a NajeriyaHoto: David Dosunmu/AP/picture alliance

Mallam Garba Shehu dai na zaman kakaki na gwamnatin da kuma ya ce Abujar na shirin zuwa ko wane matsayi da nufin kare dimukuradiyyar kasar da ke cikin barazana. Sannu a hankali dai matsalar ta tsaro ta rikide ya zuwa babban rikici na siyasa a tsakanin manyan jami'iyyun kasar guda biyu da ma yin barazana ga zaman lafiyar sassan arewacin Najeriyar da dan uwansa da ke a Kudu. A Talatar wannan makon dai, manyan hafsoshin tsaron kasar sun kare wani taron da suka faro tun daga Jumma'ar makon da ya gabata, amma kuma ba tare da nuna mataki na gaba ga masu mulkin da suke dada fuskantar matsin lamba a tsakanin al'umma.  

Karin Bayani: Boko Haram ta kafa sansaninta a Jihar Niger

Kuma a cikin wannan mako ne dai, aka tsara shugabannin majalisar dattawa za su yi tozali da shugaban kasar da nufin kallon tsaf, a cikin matsalar da ke dada sauyin launi da salo. Ibrahim Masari dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC mai mulki, da kuma ke kallon matsin lambar na kama da hassada mai zafi. Najeriyar dai na a tsakanin shawo kan mummunar matsalar rashin tsaro da bakar siyasar da ke rikidewa da kara  jefa kasar cikin tsaka mai tsananin wuya.