Farautar masu ba da kudi ga Boko Haram
March 31, 2021Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 18 ne ke hannun jami'an tsaron Tarayyar Najeriyar, wadanda ke binciken hanyoyin samar da kudi ga 'yan kungiyar Boko Haram. Gwamnatin kasar dai ta ce ta gano wasu kamfanonin canjin kudi da ke taka rawa wajen karbo kudin daga Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da mikasu ga 'yan ta'addan da ke ci gaba da tayar da hankali a Najeriyar.
Karin Bayani: Martani kan neman kudin yaki da Boko Haram
Da ma dai Hadaddiyar Daular Larabawan ta yankewa kimanin 'yan canjin shida hukunci a shekarar da ta gabata, bayan samunsu da bai wa kungiyar ta Boko Haram kudi da suka kai akalla dalar Amirka dubu 782, baya ga sababin kamun da gwamnatin kasar ta ce tai nisa a binciken da ke shirin bai wa 'yan kasar mamaki. Duk da cewar dai Abujar ba ta ambato sunaye ko kuma kamfanonin canjin ba, tun a farkon wannan mako ne dai kungiyar 'yan canji ta kasar, ta bayyana cewar jami'an tsaron cikin gida wato DSS sun kame mata 'ya'ya.
To sai dai kuma a fadar babban mashawarcin tsaron Tarayyar Najeriyar Janar Babagana Monguno gwamnatin kasar, na shirin durkusar da duk wasu masu tunanin amfani dakudin domin dakushe kokarin gwamnati na samar da zama lafiya tsakanin al'umma. Karkata zuwa ga masu samar da kudin tafi da harkoki na kungiyar dai, na zaman sabon babi a cikin yakin da ya shafe shekaru dai-dai har 12, amma kuma yafi mai da hankali zuwa ga karfi na hatsi.
Karin Byani: Tallafi ga Arewa maso Gabashin Najeriya
Kama daga kudin na waje ya zuwa harajin cikin gida dai, kungiyar na kara fadada hanyoyin samun kudin shigar 'ya'yanta, abun kuma da ga dukkan alamu ke kara mata karfin tunkarar mahukuntan Najeriyar. To sai dai kuma a fadar Kabiru Adamu da ke zaman masanin harkar tsaro datse kudi ga kungiyar ta Boko Haram, na kara taimakawa ya zuwa kai 'yan dinkin hular zuwa gidan tarihi a lokaci kankani. Tun a shekara ta 2016 ne dai, kasar Hadaddiyar Daular Larabawan ta fara bin diddigin kudin kungiyar da ke badda sahu daga Turkiya, sannan ya kare a ofisoshin 'yan canjin a birane dabam-dabam cikin Tarayyar Najeriyar.