SiyasaAsiya
Pakistan ta amince da takarar tsohon Firaminista Nawaz
December 28, 2023Talla
Sai dai har yanzu Sharifna bukatar a cire masa dokar da ta haramta masa rike duk wani mukami na gwamnati domin ya cancanci tsayawa takara, don haka ba a bayyana yadda aka amince da bashi damar yin takarara ba.
A shekarar 2017 ne dai kotun kolin Pakistan ta dakatar da Sharif shiga zabe, saboda dalilai na rashin gaskiya wajen bayyana yawan kudaden shigar wani kamfani mallakar dansa.
Sharif, wanda ya dawo gida a watan Oktoba dagagudun hijirar-kashin-kaina tsawon shekaru hudu a London, yana neman tsayawa takara karo na hudu a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Fabrairu.