1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sahel: Hare-hare a makarantu ya karu

Abdourahamane Hassane LMJ
September 9, 2020

A karon farko Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar tara ga watan Satumba domin yaki da hare-hare da kungiyoyin masu dauke da makamai ke yi a kan dalibai da malamai da ma makarantu.

https://p.dw.com/p/3iDgG
Bombenexplosion in Maiduguri Nordnigeria 2013
Hare-haren ta'addanci na kassara harkokin koyo da koyarwa a yankin SahelHoto: picture-alliance/dpa/D. Yake

Cikin rahoton da hadin gwiwar kungiyoyin wato Global Coalitaion to Protect Education from Attack GCPEA suka fitar, sun nunar da cewa hare-haren a makarantu a kasahen yankin na Sahel ya ninka har sau biyu, tun daga shekara ta 2018 zuwa 2019. Rahoton kungiyar da ke da cibiya a birnin New York na Amirka dai, ya nunar da cewa tsakanin watan Janairu da Yuli na shekara ta 2020 sama da hare-hare 85 kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai a Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, duk kuwa da cewa an rufe makarantu zuwa wani lokaci sakamakon annobar COVID-19.

To amma a lokacin da aka sake bude makarantun domin bayar da dama ga 'yan makaranta don yin jarabarwa karshen shekara kimanin hare-hare 27 aka kai a makarantu da kwaleji a Mali, yayin da aka kai wasu hare-haren guda 60 a kan makarantun firamare.

 Karin Bayani: Sahel : Rundunar hadaka da Turai a Mali

Hare-haren dai sun janyo an ruife makarantu sama da 1,100 a Mali. Marika Tsolakis mai yin bincike a kan hare-haren a hadin gwiwar kungiyoyin na GCPEA, ta bayyana yadda suka tantance alkaluman lissafin: "Muna gudanar a bincike a kan sha'anin ilimi a jumulce, muna da mutane da ke kusan dukkanin kasahen Sahel. inda lamarin ke faruwa wadanda ke bin kadi suna yi mana kididdiga. Sanan muna aiki da rahoton kungiyoyi masu zaman kansu da na Majalisar Dinkin Duniya da ma na kafofin yada labarai."

Mali Symbolbild Bildung
Dalibai da malan makarantu na cikin hadariHoto: picture-alliance/AP Photo/UNICEF/Dicko

Yawanci kungiyoyi masu aikin ta'addanci da ke kai hare-haren, sun fi kai wa a makarantun gwamanati tare da kashe malaman makarantar da yin fyade ga malamai mata da ma 'yan makaranta da kuma yin garkuwa da wasu ko ma kashe su. Akasari  dai sakamakon fyaden, wasu matan kan samu juna biyu ba cikin shiri ba wanda hakan kan sa wasu 'yan matan sam ba za su sake komawa makarantar ba.

 Karin Bayani: Yunkurin tabbatar da tsaro a wasu kasashen Sahel

Hadin gwiwar kngiyoyin  na GCPEA sun yi kira ga kasashen duniya wadanda suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar kare dalibai da malamai da makaranmtun boko  da jami'o'i ko da a lokacin yaki, kan su kara daukar matakai na kiyaye faruwar haren-haren ko da kuwa ta hanyar rufe makarantun ne, idan aka yi la'akari da cewar wani bangaren yankin na Sahel na cikin hadari na fuskantar hare-hare a makarantu.

Karin Bayani: Taro kan matsalar tsaro a Nijar

A rahaton dai kungiyoyin sun ce a duniya baki daya tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2019, an kai hare-hare sama da ubu 11 a cikin makarantu da ya shafi malamai 'yan makaranta, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai da malamai dubu 22.