1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce ta tarwatsa wata makarkashiya daga Ukraine

December 27, 2024

Fadar mulki ta Kremlin a Rasha, ta ce ta wargaza wani shiri da Ukraine ta yi na kashe mata wasu manyan jami'ai. Gagarumin rikicin Rasha da Ukraine dai ya doshi shekaru uku ne a yanzu.

https://p.dw.com/p/4obnz
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir PutinHoto: Gavriil Grigorov/POOL/AFP

Fadar mulki ta Kremlin a Rasha, ta ce ta wargaza wani shiri da Ukraine ta yi na kashe mata wasu manyan jami'ai.

Hukumar leken asiri ta Rashar wato KGB ta ce ta ma kama wasu 'yan kasar su hudu da aka kulla makarkashiyar kai wasu hare-hare.

A cewar hukumar ta ma kai ga wani daga cikin wadanda ta kaman, ya makala bam karkashin motar wani jami'in hukumar tsaron kasar.

Akwai ma wani da ake zarginsa da mika wani bam din da ya kunshe a matsayin kyauta ga wani jami'in tsaro a Rasha.

To sai dai babu wani bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da gaskiyar ikirarin na hukumomin Rasha da suke dora laifi a kan Ukraine.

Wannan lamari dai na zuwa ne mako guda bayan mutuwar wani babban jami'in da ke kula da nukiliyar Rasha a kofar gidansa bisa zargin makala masa bam a jikin wani keke mai amfani da lantarki.