1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Butaniya ta ce Rasha ta tafka asarar dubban sojoji a Ukraine

November 10, 2024

Burtaniya ta ce Rasha na tafka asara mai yawa a yakin Ukraine. Kudaden dai da Rashar ke barnatarwa a yakin, na matukar tasiri a karfinta na tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4mqzZ
Tony Radakin, babban hafsan tsaro a Burtaniya
Tony Radakin, babban hafsan tsaro a BurtaniyaHoto: ayfun Salci/ZUMA/picture alliance

Babban hafsan tsaron kasar Burtaniya, Admiral Tony Radakin ya ce Rasha na tafka asara mai yawa a yakin nan da ta ke yi a Ukraine.
A cewar Admiral Tony Radakin, kimanin sojoji dubu da 500 rundunar sojin Rasha ta yi asarar su a kullum a Ukraine a cikin watan jiya.

Babban jami'in sojin na Burtaniya, ya ce watan na jiya wato Oktoba, ya kasance mafi asara ga Rasha a dai tsawon lokacin da ta afka wa Ukraine din da yaki.

Baki daya dai a cewar Admiral Tony Radakin, Rasha ta yi asarar dakaru dubu 700 a tsakanin wadanda suka mutu da ma suka jikkata.

Radakin ya kuma ce yayin da Rasha ke nasarar dora wa Ukraine tsananin matsi, asarar da take tafkawa daga nata banagren duk tana yin su ne saboda neman dan kankani fili da take son ta mamaye na Ukraine.

Kudaden dai da Rashar ke barnatarwa a yakin, suna matukar na matukar tasiri a karfinta na tattalin arziki.