1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Habasha da Masar sun gaza cim ma matsaya kan Kogin Nilu

December 21, 2023

An tashi a taron neman sasanta rikicin da ke tsakanin Masar da Habasha game da madatsar ruwan nan na kogin Nilu ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

https://p.dw.com/p/4aQX0
Madatsar ruwa ta Kogin Nilu da ake takaddama a kai
Madatsar ruwa ta Kogin Nilu da ake takaddama a kaiHoto: Minasse Wondimu Hailu/AA/picture alliance

Kasashen na Habasha da Masar dai sun tashi ne baram-baram kowa na zargin dan uwansa, a taron da suka kwashe kwanaki uku suna yi a birnin Addis Ababa.

Ministan albarkatun ruwa na Masar ya ce rashin nasara a taron ya faru ne saboda bijire wa duk wani batu na sulhu da Habasha ta yi.

Yayin kuma da ita ministan harkokin wajen Habasha daga nashi bangaren ya ce Masar ce ta sanya tarnakin da ya hana kai su ga cim ma masalaha.

Masar dai na fargabar iya samun matsaloli idan har madatsar ta fara aiki, inda take bukatar Habasha ta sanya bukatunta a ciki.

Kasar Sudan dai na cikin wadanda ke shiga tsakani a dambarwar da ke tsakanin kasashen biyu.