1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yakin Gaza: Sakatare Janar na MDD na ziyara a Masar

March 23, 2024

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya isa Masar a shirye-shiryen zuwa kan iyakar Rafah da ke tsakanin Masar da Zirin Gaza da Isra'ila ke ci gaba da luguden bama-bamai babu kakkautawa.

https://p.dw.com/p/4e3YX
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres tare da tawagar gwamnatin Masar a yayin da ya isa filin jirgin saman Al-Arish dake kan iyakar Rafah a Masar.
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres tare da tawagar gwamnatin Masar a yayin da ya isa filin jirgin saman Al-Arish dake kan iyakar Rafah a Masar.Hoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Guterres zai yi ziyarar gani da ido da kuma tattaunawa da ma'aikatan dake ayyukan jinkai a yankin, a daidai lokacin da ma'aikatar lafiyar Zirin Gaza ke sanar da alkaluman mutune dubu 32,142  da suka mutu tun bayan fara yakin da galibinsu mata ne da kananan  yara.

Karin bayani: MDD ta bukaci da a dakatar da Isra'ila daga kai hari a Rafah 

Duk da kiraye-kirayen tsagaita bude wuta da kuma matsin lamba daga kasashen duniya, Firaimistan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba zai saurara ba har sai hakarsa ta cimma ruwa na murkushe mayakan Hamas.

Karin bayani: Kotun duniya ICJ za ta fara sauraron shari'ar halascin mamayar da Isra'ila ta yi wa Falasdinawa

Ziyarar ta Guterres na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kwana ta shida a gumurzun da ake tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas masu dauke da makamai a harabar asibitin Al Shifa da ke tsakiyar birnin Gaza.